Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Manchester City ta kashe Euro biliyan 1 kan tawagarta

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da ke Ingila ta hada tawagar ‘yan wasa da ta kai ta Yuro bilyan daya, kungiya ta farko da ta yi haka, in ji wani rahoto.

Wasu 'yan wasan Manchester City lokacin da suka lashe kofin Community Shield karo na biyu a jere
Wasu 'yan wasan Manchester City lokacin da suka lashe kofin Community Shield karo na biyu a jere AFP/Adrian Dennis
Talla

City, wacce ta ci moriyar karbar kungiyar da kamfanin Abu Dhabi ya yi tun a shekarar 2008 ta kashe Yuro biliyan daya da miliyan 14 kan ‘yan wasanta, wato kwatankwacin fam miliyan 906 kenan, yayin da Paris Saint Germain ta Faransa ta kashe Yuro miliyan 913, a matsayi na biyu, Real Madrid ta Spain, a matsayi na uku ta kashe yuro miliyan 902.

Darajar abin da aka kashe kan ‘yan wasan Manchester City ta ninka ta kungiyar kwallon kafa ta Norwich har sau 32.

CIES, wato kungiyar da ta yi wannan bincike, wacce ke kasar Switzerland, ta yi nazari ne kan manyan ‘yan wasa dake manyan gasannin lig – lig na Turai hudu, wato Premier League, La liga, Serie A da Bundesliga.

Paderborn, kungiyar kasar Jamus da ta samu ci gaba zuwa babban gasa a wannan kaka, ita ce mai tawaga mafi araha, na fam miliyan 3 da dubu 57.

Kungiyoyi 10 na farko da darajarsu a kudin Yuro:

1. Manchester City - 1.014 billion

2. Paris St-Germain - 913m

3. Real Madrid - 902m

4. Manchester United - 751m

5. Juventus - 719m

6. Barcelona - 697m

7. Liverpool - 639m

8. Chelsea - 561m

9. Atletico Madrid - 550m

10. Arsenal - 498m

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.