Isa ga babban shafi
Rasha-Faransa

Macron ya yabawa Putin kan musayar Fursunoni da Ukraine

Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaran sa na Faransa Emmanuel Macron sun yaba da musayar fursunonin da Rasha ta yi da Ukraine a karshen mako, a tattaunawar da suka yi ta waya.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin ganawarsa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a Faransa.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin ganawarsa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a Faransa. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Tattaunawar na zuwa ne kafin ziyarar da ministan harkokin wajen Faransa da takwaran sa na tsaro za su kai Rasha domin ganawa da hukumomin kasar.

A watan jiya, shugaba Macron ya gana da Putin a Faransa inda ya bukaci gaggauta kawo karshen rikicin Rasha da Ukraine da aka kwashe shekaru 5 ana yi.

Fadar Kremlin ta ce shugabannin biyu sun bayyana farin cikinsu da musayar firsinonin 35.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.