Isa ga babban shafi
Birtaniya

Brexit: Yan Birtaniya na zanga-zanga kan dakatar da majalisa

Dubban ‘yan Birtaniya sun gudanar da zanga-zanga a sassan kasar, don nuna adawa da matakin Fira Minista Boris Johnson, na dakatar da aikin majalisar kasar har sai ya rage makwanni biyu su fice daga cikin kungiyar tarayyar Turai, ranar 31 ga watan Oktoba.

Masu zanga-zangar adawa da Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson.
Masu zanga-zangar adawa da Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson. © REUTERS/Henry Nicholls
Talla

Zanga-zangar a Birtaniya ta zo ne yayinda bangaren ‘yan adawa ke shirin kalubalantar matakin na Fira Minista Boris Johnson a kotu, da kuma shirya kada kuri’ar yankar kauna kan gwamnatinsa a zauren majalisar kasar cikin mako mai kamawa.

Taro mafi girma yayin zanga-zangar ta yau a sassan kasar ta Birtaniya dai na gudana ne a birnin London, sai kuma Manchester, Newcastle, Edinburgh da kuma Belfast, sai kuma karin wasu sassa akalla 30.

A baya bayan nan Fira Minista Boris Johnson yayi gargadin cewa ba zai lamunci duk wani yunkuri daga wasu ‘yan majalisar kasar ba, da suka daura aniyar dakatar da ficewar Biraniya daga daga cikin kungiyar EU, ko kuma tsawaita wa’adin kammala rabuwarsu na ranar 31 ga watan Oktoba.

Johnson ya ce muddin ‘yan majalisun kasar suka cimma nasarar aiwatar da wannan aniya, to fa ba shakka ‘siyasar Birtaniya za ta rasa kima da amincewa daga yan kasar, la’akari da cewa sun ne suka zabi ficewa daga cikin kungiyar kasashen Turai a shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.