Barca na ci gaba da tattaunawa da PSG
Magabatan kungiyoyin Barca da na Paris Saint Germain na ci gaba da tattaunawa bayan wata yar gajeriyar ganawa a jiya talata tsakanin su dangane da batun sayar da dan wasan Brazil Neymar zuwa tsohuwar kungiyar sa ta Barca.
Wallafawa ranar:
An dai safe makwonni ana tattaunawa tsakanin bangarorin wanda ake kuma ganin cewa ganawar ta jiya talata na tabbatar da ficewar dan wasan zuwa Barcelonna.
A cewar wata jarida mai suna le Parisien, wannan jarida ta tsegunta cewa kungiyar Barca ta shirya domin sayen dan wasan a kan kudi Milyan 170 na Euros.
Kudin da zata biya sau biyu a cewar jaridar tareda bayar da wani dan wasa bayan haka.
A jiya talata an hango Oscar Grau tareda rakiyar Eric Abidal da wasu mukaraban kungiyar ta Barca da suka shiga tattaunawa da Leonardo mai kula da bangaren motsa jiki a kungiyar ta Paris Saint Germain.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu