Isa ga babban shafi
Netherlands

Kamfanoni 100 sun yi kaura daga Birtaniya saboda Brexit

Kimanin manyan kamfanonin kasa da kasa 100 ne suka koma Netherlands daga Birtaniya, yayinda 325 ke shirin ficewa nan kusa sakamakon fargabar makomar tattalin azikin kasar bayan kammala ficewarta daga Kungiyar Tarayyar Turai.

Alamu na nuna cewa, watakila Birtaniya ta fice daga gungun kasashen Turai ba tare da yarjejeniya
Alamu na nuna cewa, watakila Birtaniya ta fice daga gungun kasashen Turai ba tare da yarjejeniya REUTERS/Hannah Mckay
Talla

Hukumar Kula da Zuba Hannayen Jarin Kasashen Ketare ta Netherlnad, NFIA ta ce, kamfanoni da masana’antun Birtaniya na nuna sha’awarsu ta komawa kasar.

Shugaban Hukumar ta NFIA, Jeroen Nijland, ya ce, kamfanonin na yin kaura daga Biraniya sakamakon fargabar makomar tattalin arzikinta a daidai lokacin da alamu ke nuna cewa, akwai yiwuwar ta raba gari da Kungiyar Tarayyar Turai ba tare da cimma wata yarjejeniya ba.

Wannan ne babban dalilin da ya sa kamfanonin ke komawa Netherlands domin zama sabuwar cibiyar kasuwancinsu a Turai. In ji Nijland.

Tuni dai kamfanoni 62 suka samar da guraben ayyukan yi har guda 2,500 a Netherlands bayan sun yi kaura daga Birtaniyar, sannan kuma suka zuba jarin da ya kai Euro miliyan 310.

A yanzu haka, kasar ta Netherlands za ta ci gaba da gogayya da manyan kasashen Turai da suka hada da Faransa da Jamus da Belgium da Ireland wajen zawarcin kamfanonin Birtaniya da ke ficewar daga kasar saboda Brexit.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.