Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa na bikin cika shekaru 75 da murkushe dakarun Nazi

Yau Faransa ke bikin cika shekaru 75 da kawo karshen mamayar da dakarun sojin Nazi, karkashin Adolf Hitler na Jamus, suka yiwa birnin Paris.

Dakarun kawancen kasashen Turai a harabar fadar Champs Elysées Avenue dake Paris, yayin faretin murnar nasarar murkushe sojojin Nazi na Jamus, dake karkashin Adolf Hitler yayin yakin duniya na biyu.
Dakarun kawancen kasashen Turai a harabar fadar Champs Elysées Avenue dake Paris, yayin faretin murnar nasarar murkushe sojojin Nazi na Jamus, dake karkashin Adolf Hitler yayin yakin duniya na biyu. AFP
Talla

A rana mai kamar ta 25 ga watan Agustan 2019, cikin shekarar 1944, dakarun Faransa da hadin gwiwar ma’aikata, mata, har ma da limaman COCI suka samu wannan nasara bayan shafe kwanaki 6 suna gwabza fada da dakarun na Nazi.

Ranar 6 ga watan Yuni na shekarar ta 1944, rundunonin sojin Amurka, Birtaniya da kuma Canada da suka kaddamar da farmakin hadin gwiwa kan dakarun na Nazi dake karkashin jagorancin Adolf Hitler na Jamus.

Bayan shafe makwanni ana gwabzawa ne kuma a ranar 25 ga watan Agustan na 1944, Janar Charles de Gaulle yayi shelar nasarar murkushe sojojin na Nazi, bayan samun agajin dakarun na kawance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.