Isa ga babban shafi
Faransa-Birtaniya

Macron ya amince da karin kwanaki kan ficewar Birtaniya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nuna goyon bayansa ga karin kwanaki 30 na tattaunawa kan ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai, a wata ganawa da ya yi da Firaministan Birtaniya, Boris Johnson.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Boris Johnson na Birtaniya
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Boris Johnson na Birtaniya hristophe Petit Tesson/Pool via REUTERS
Talla

Kamar yadda shugabar Jamus Angela Merkel ta yi a ranar Laraba, Macron ya goyi bayan karin wasu kwanaki 30 don lalubo mafita game da batun da ya shafi iyakar Ireland, wanda shi ya yi wa tattaunawar kafar ungulu tun shekarar 2017.

Sai dai shugaban na Faransa wanda ya ce, ya yi kaurin suna saboda matsayinsa kan ficewar Birtaniya daga kungiyar Turai, ya yi watsi da bukatar Johnson ta soke matsayar da aka cimma tsakannin tsohuwar Firaminista Theresa May da Kungiyar Tarayyar Turai game da yankin Ireland.

Batun dai da ke janyo kiki–kaka shi ne, janye dukkannin shamaki a kan iyakar Ireland da zai hana dawowar binciken kan iyaka tsakanin Ireland da Arewacin Ireland wacce ke karkashin ikon Birtaniya.

Yayinda Johnson ke ganin janye wannan shamaki karan-tsaye ne ga dokoki da ma mutuncin Birtaniya a matsayin ‘yantattar kasa, Tarayyar Turai na jin cewa maido da binciken zai dawo da rikici a tsakanin yankunan biyu, inda tarzomar kin jinin Birtaniya ta lakume dubban rayuka.

Tun da Boris Johnson ya dare kan karagar mulki a watan jiya, batun ficewa daga Kungiyar Turai ba tare da yarjejeniya ba, ya dada kamari, abinda masana tattalin arziki ke ganin zai kawo nakasu ga tattalin arzikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.