Isa ga babban shafi
Italiya

Firaministan Italiya zai yi murabus bayan rincabewar rikicin siyasa

Bayan caccakar Matteo Salvini ministan cikin gidan Italiya game da rikicin siyasa da tabarbarewar tattalin arzikin kasar, Firaministan Italiyan Giuseppe Conte ya bayyana aniyar yin murabus, ya na mai dora alhakin matsalolin kasar kan Salvini wanda ya zarga da nuna son zuciyar da ya haddasawa kasar matsalaloli.

Firaministan Italiya Giuseppe Conte yayin jawabinsa gaban zaman majalisar kasar
Firaministan Italiya Giuseppe Conte yayin jawabinsa gaban zaman majalisar kasar REUTERS/Yara Nardi
Talla

Bayan ya shafe kusan sa a guda yana jawabi ga majalisar dattawan kasar, Conte ya ce la shakka zai zai yi murabus, kuma zai shaida wa shugaban kasar, Sergio Mattella aniyarsa.

Conte ya bayyana haka ne bayan mako daya na kai-ruwa-rana sakamakon matakin Salvini na janyewa daga hadin gwiwa tsakanin jam’iyyarsa da Five Star Movement mai adawa da gwamnati a ranar 8 ga watan Agusta, lamarin da ya jefa kasa ta uku mafi karfin tattalin arziki a Turai cikin rikicin siyasa.

Bayan da Conte ya sanar da aniyar murabus ne dai, shugabar majalisar kasar Elizabette Casellati ta umarci Salvini ya tashi daga bangaren gwamnati tare da komawa bangaren sanatocinsa, ba kuma tare da nadama ba, ministan cikin gidan na Italiya ya aikata abin da aka umarce shi, ya na mai cewa a shirye ya ke ya maimaita abin da ya aikata.

A makon da ya gabata Salvini ya dau mataki mai ban mamaki na goyon bayan bukatar jam’iyyar M5S na rage yawan ‘yan majalisar dattawa daga 950 zuwa 605, amma fa sai idan za a yi gaggawar gudanar da zabuka.

Karshen wannan gwamnati da ta yi tashen watanni 14 ya baiwa shugaba Matarella damar tuntubar jam’iyyun siyasa da jerin zabi da dama, ciki har da na ko a gudanar da zaben gaggawa, ko wata gwamnatin hadin gwiwa, ko kuma kila wa kala, barin wannan gwamnatin ta ci gaba da wanzuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.