Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya gana da Putin kan rikicin Ukraine

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya karbi bakuncin takwaransa na Rasha Vladmir Putin, gabannin taron kasashen kungiyar G7.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, yayin ganawa da takwaransa na Rasha Vladmir Putin a Biarritz dake Faransa.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, yayin ganawa da takwaransa na Rasha Vladmir Putin a Biarritz dake Faransa. Gerard Julien/Pool via REUTERS
Talla

Ziyarar ta Putin a Faransa, na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki 5 shugabanin kasashen G7 su soma taron kwanaki biyu daga ranakun 24 zuwa 26 na watan Agustan da muke ciki, a Biarritz dake Faransa.

Yayin ganawar, shugaba Macron ya yi amfani da damar wajen gamsar da Putin ya amince da tayin Ukraine na tattaunawa kan rikicin gabashin kasar da yankin Crimea.

Bayan kammala ganawar shugabannin biyu, sun amince da shirya wani taro na musamman da zai samar da matakan warware rikicin Ukraine da Rasha.

Sai dai an gaza samun matsaya guda tsakanin Macron da kuma Putin, dangane da yakin Syria, inda Faransa ke sukar hare-haren da kawancen sojin kasar ta Syria da na Rasha ke kaiwa yankunan da suka rage a karkashin ikon 'yan tawaye, lamarin dake ci gaba da haddasa hasarar rayukan fararen hula.

A shekarar 2014 kasashen G7 suka kori Rasha daga cikinsu, a lokacin da suke amsa sunan kasashen kungiyar G8 mafiya karfin tattalin arziki, bayanda da Rashar ta mamaye yankin Crimea, mamayar da kasashen duniya suka bayyana a matsayin haramtacciya.

Jim kadan bayan mamaye yankin na Crimea ne kuma yaki ya barke a gabashin Ukraine tsakanin mayakan ‘yan aware da Rasha ke marawa baya, da dakarun gwamnati, rikicin da yayi sanadin halakar akalla mutane dubu 13,000.

Sai dai a baya bayan nan, shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya sha alwashin kawo karshen rikicin kasashen biyu, tare da samun kwarin gwiwar cimma burin daga sabon shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, wanda a makwannin da suka gabata, ya bukaci tattaunawar kai tsaye da Vladmir Putin, bayan ganawar da yayi da shugaban na Rasha ta wayar tarho.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.