Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya jajanta wa iyalan wadanda harin bindiga ya shafa

Shugaban Amurka Donald Trump ya jajantawa iyalai da kuma wadanda hare-haren ‘yan bindiga ya ritsa da su a jihohin Texas da Ohio.A wannan Laraba Trump yayi tattaki zuwa Dayton da El Paso, yankunan da ‘yan bindiga suka halaka mutane 29.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Leah Millis
Talla

Shugaban na Amurka Donald Trump da mai dakinsa Melania sun shafe mafi rinjayen lokacin ziyarar da suka kai, wajen janjantawa wadanda suka jikkata a hare-haren ‘yan bindigar da kuma iyalansu a Dayton da mutane 9 suka halaka, da kuma El Paso da dan bindigar ya yi wa mutane 22 kisan gilla.

Yayin ziyarar dai Trump ya fuskanci suka daga al’ummar yankunan da kuma sauran ‘yan adawa, da ke zarginsa da karfafa dabi’ar kyamar baki da fifita turawa fararen fata, sakamakon kalaman da shugaban ya sha furtawa masu alaka da batututwa musamman kan bakin-haure ko ‘yan ci rani da ya taba kira da ‘yan mamaya.

Sai dai a lokaci guda dimbin magoya bayan shugaban na Amurka su ma sun gudanar da na su gangamin na nuna masa goyon baya.

Ta’addancin da ‘yan bindiga suka yi a bayan bayan nan a jihohin Texas da Ohio, yasa sake tayar da muhawara tsakanin masu neman samar da dokokin takaita mallakar bindiga ko ma hanawa da masu adawa da bukatar.

Sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayi da aka yi a watan Mayu ya nuna cewa 63 daga cikin adadin Amurkawan da aka tuntuba suna goyon bayan haramta mallakar bindiga a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.