Isa ga babban shafi
Faransa

Kotun Faransa ta daure matashiyar 'yar ta'adda

Wata Kotun Faransaa ta zartar da hukumcin daurin shekaru 7 kan matashiyar nan da aka cutsawa tsatsauran ra’ayi har ta yi kokarin kai harin ta’addanci a karkashin Kungiyar ISIS a shekarar 2016 a kasar.

Faransa ta fuskanci hare-haren 'yan ta'adda da suka hallaka mutane da dama
Faransa ta fuskanci hare-haren 'yan ta'adda da suka hallaka mutane da dama REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Kotun ta zartar mata da wannan hukunci da ya kunshi zaman gidan yari na shekaru 2 a tsare, a yayinda sauran shekaru 5 kuma za a zuba ido a kanta.

A ranar 12 ga watan Yulin da ya gabata ne, mai shigar da karar gwamnatin Faransa ya bukaci zartar wa matashiyar mai shekaru 21 a duniya hukuncin daurin zama gidan yari na tsawon shekaru 10.

Ita dai wannan matashiya da aka jirkitawa tunani kwana daya kafin kama ta, ta gudanar da bincike ta shafin yanar gizo domin gano yadda ake hada damarar bama-bamai.

A kafar sadarwar Snapchat kuma, matashiyar ta rubuta sakon da ke cewa, sai mun hadu a aljanna ta har abada.

Matashiyar dai ta sanar da kotun cewa a wancan lokacin da ta aikata haka, tana cikin duhun jahilci ne, wanda ya sa take kallon kai harin ta’addanci a a matsayin wani karamin abu mai sauki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.