Da misalin karfe 8 da da mintuna 17 ne Zapata ya yi nasarar tashi akan injin na sa, inda ya yi tafiyar mintuna 22 a sararin samaniya, kafin daga bisani ya sake tashi tun daga kasar ta Faransa zuwa Birtaniya.
Rahotanni sun bayyana cewa Injin tashi saman na Zapata na gudun kilomita 160 zuwa 170 a sa’a guda.
10 da suka gabata dai Zapata ya yi nasarar tashi a kan injin na sa amma kuma ya yi rashin nasarar fadawa teku.