Isa ga babban shafi

Macron ya gargadi Johnson kan ficewar Birtaniya daga EU

Shugban Faransa Emmanuel Macron ya gargadi sabon Firaministan Birtaniya Boris Johnson kan ya kaucewa daukar duk wani mataki ko furta kalaman tunzuri, game da shirin kasar na ficewa daga cikin kungiyar EU. Gargadin na zuwa ne gabannin ziyarar da ake sa ran Johnson zai kai Faransa nan da 'yan makwanni masu zuwa.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Ludovic MARIN / AFP
Talla

Har yanzu dai babu karin bayani kan lokacin da aka tsara ganawar shugaban na Faransa da Firaministan na Birtaniya Boris Johnson, da zai ziyarci kasar ta Faransa daga ranakun 24 zuwa 26 na watan Agustan da ke tafe,domin halartar taron kungiyar kasashen G7 masu karfin tattalin arziki a duniya.

A jiya Alhamis kungiyar tarayyar Turai ta yi watsi da bukatar Firaministan Johnson kan yiwa yarjejeniyar Brexit da kungiyar kasashen Turai ta cimma da tsohuwar Firaminista Theresa May, wadda ya bayyana ta a matsayin illa ga tattalin arzikin Birtaniya, dan haka idan har sake tattaunawa kan ka’idojin bai yiwu ba, basu da zabi illa ficewa daga cikin kungiyar kasashen Turan ba tare da cimma wata yarjejeniya ba a ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa.

A baya bayan nan ma dai ministan harkokin wajen Ireland da ke karkashin Birtaniya, mai goyon bayan ci gaba dazama tare da EU, Simon Coveney ya zargi Boris Johnson da shirya haifarda rudani kan yarjejeniyar Brexit da gangan, la’akari da irin kalaman da yake furta da kuma matsayar daya dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.