Isa ga babban shafi
Turkiya-Gulen

Turkiya na neman karin mutane 122 masu hannu a yunkurin juyin mulki

Rahotanni daga Turkiya na cewa jami’an a sanda a sassa daban daban na kasar sun gudanar da sumame don lalubo wasu mutane 122 da ke da hannu a yunkurin juyin mulkin kasar na 2016 da bai yi nasara ba.

Shugaban Turkiya Recep Dayyib Erdogan
Shugaban Turkiya Recep Dayyib Erdogan REUTERS/Murad Sezer
Talla

Kamfanin dillancin labaran Turkiyan ya bayyana cewa kotunan birnin Santanbul ne suka bayar da umarnin kame mutanen su 122 ciki har da sojoji da ke bakin aiki da kuma wasu da aka dakatar tun a wancan lokaci, galibi a yankunan Konya da Izmir.

Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka an kame akalla mutane 41 inda su ke hannun hukuma kafin fara fuskantar tuhuma a gaban Kotu.

Tun bayan yunkurin na hambarar da shugaba Recep Tayyib Erdogan a 2016, fiye da mutane dubu 140 aka kora daga aiki yayinda aka kame daruruwa bisa zarginsu da alaka da fitaccen malamin addinin kasar mazaunin Amurka wanda Erdogan ke zargi da kitsa juyin mulkin, zargin da Gulen ke ci gaba da musawa tsawon lokaci.

Ko cikin watan jiya, Ankara ta yankewa daruruwan mutane hukuncin daurin rai da rai wasu kuma na tsawon shekaru duk dai kan zargin hannunsu a yunkurin juyin mulkin, matakin da ya janyo mata tsamin alaka da makotanta kasashen turawan yamma.

Kasashen Turai dai na zargin Turkiya da kame bangarorin adawa tare da garkame su bisa kafa hujja da cewa suna da hannu a juyin mulkin.

Sai dai Shugaba Recep Tayyib Erdogan ya sha alwashin cewa ba zai dakata da kamensa ba har sai ya kammala kakkabe masu biyayya ga Gulen a fadin Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.