Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Tsananin zafi ya tilasta takaita zirga-zirga a nahiyar Turai

Hukumomin Kasashen Turai sun gargadi mazauna yankin da su kiyaye barazanar da ke tattare da tsanani zafin da ake fuskanta yanzu haka wanda ake ganin zai zarce maki 40 a ma’aunin salsiyas.

Tsananin zafin ya tilastawa Jama'a tururuwa bakin teku don samun sauki
Tsananin zafin ya tilastawa Jama'a tururuwa bakin teku don samun sauki REUTERS/Heino Kalis
Talla

Zafin ya sa an takaita zirga zirgan ababan hawa inda a bangare guda ya ke haifar da gobarar daji a wasu yankunan Nahiyar, yayinda kuma tsananin zafin ya haifar da cacar baki kan yadda wasu ke tafiya tsirara.

A Spain hukumomi na gargadin cewar zafi na iya kai wa maki 42 zuwa 50 a wasu sassan kasar, yayin da ake saran ganin maki 44 a Italia da kuma maki 40 a Faransa.

Ko a bara ma dai tsananin zafin ya yi mummunar illa ga nahiyar ta Turai inda a wasu kasashen aka haramta gashe-gashen nama da sauran abubuwan da za su kara zafin gari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.