Isa ga babban shafi
Birtaniya

'Yan takarar maye gurbin Theresa May sun ragu a Majalisar Birtaniya

‘Yan takaran da ke neman maye gurbin Firaministan Birtaniya, Theresa May sun ragu zuwa 5 daga 6, kamar yadda suke tun a makon da ya gabata, bayan zabe zagaye na biyu, wadda tsohon ministan harkokin wajen kasar, Boris Johnson ke kan gaba.

Zaman kada kuri'a tsakanin 'yan takarar Firaministan Birtaniya a Majalisar Kasar
Zaman kada kuri'a tsakanin 'yan takarar Firaministan Birtaniya a Majalisar Kasar HO / PRU / AFP
Talla

Boris Johnson ya samu kuri’u 126 daga kuri’u 313 da aka kada a karamar majalisar dokokin Birtaniya, yayin da wani tsohon minista, Domic Raab ya rikito daga takarar.

Shi ko ministan harkokin wajen kasar mai ci, Jeremy Hunt kuri’u 46 ya samu, yayin da ministan muhalli Michael Gove ya samu kuri’u 41, ministan bunkasa kasashe Rory Stewart ya tsahi da kuri’u 37, sai minikstan cikin gida, Sajid Javid ya samu 33.

Rinjayen da Boris Johnson ke da shi a wannan takara dai gagarumi ne, inda har wasu kafafen yada labaran Birtaniya na cewa sauran ‘yan takaran na harbin iska ne kawai, saboda sun san ba za su kai labari ba, don haka kokartawa suke ko za su samu wuri mai danshi idan Johnson ya kafa gwamnati.

Birtaniya na dai na dakon wanda zai ja ragamar shugabancin kasar, tun bayan da Firaminista Theresa May ta yi murabus a watan jiya bayan kokarinta na kai kasar ga ficewa daga Tarayyar Turai ya ci tura.

Kuri’ar da za a kada a ranakun Laraba da Alhamis za su rage yawan 'yan takarar zuwa 2 inda daga nan ne kuma za a sake zabe tare da tantance wanda zai zamo Firaminista na gaba.

A ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa ne ake saran Birtaniyar ta raba gari da takwarorinta kasashen Turai 27, dai dai lokacin da rikicin siyasa da na kasuwanci ya dabaibaye kasar a bangare guda kuma 'yan kasuwa ke razane da kasar kan makomar kasuwancinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.