Isa ga babban shafi
Faransa

Watakila Sarkozy ta gurfana a gaban kotu

Akwai yiwuwar tsohon shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy ya gurfana gaban kotu a cikin ‘yan watanni masu zuwa bayan ya yi rashin nasara a daukaka karar da ya yi, don kauce wa tuhumar da ake masa kan rashawa da karya ka’idar kashe kudade a yayin yakin neman zaben shugaban kasa.

Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy
Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy REUTERS/Charles Platiau/File Photo
Talla

Kotun daukaka kara a Faransa  ta yanke hukuncin cewa, Sarkozy ya cancanci a gurfanar da shi gaban kotu don ya fuskanci tuhumar da ake masa da lauyansa Thierry Herzog da tsohon alkali Gilbert Azibert.

Hakan na nufin kenan za a ci gaba da shari’ar tsohon shugaban kasar na Faransa, kamar yadda wata majiya ta kusa da kotun da daya daga cikin lauyoyin wanda ake tuhumar suka bayyana.

Ana tuhumar Sarkozy ne da karbar wasu makudan kudade daga wani kamfani don gudanar da yakin neman zabensa, sannan kuma ya yi amfani da takardun shaidar kashe kudade na bogi a shekarar 2007.

Gabanin wannan hukuncin an wanke Sarkozy kan batun a shekarar 2013 bayan daukaka karar da ya yi, abinda ke nufin ba zai fuskanci shari’a ba.

Masu gabatar da kara sun yi zargin cewa, Sarkozy ya kashe kusan Yuro miliyan 43 a yakin neman zabensa, abinda ya kusan ninka ainihin kudin da aka amince a kashe wato Yuro miliyan 22.5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.