Isa ga babban shafi

Sharapova za ta dawo fagen tennis bayan jinya

Ana sa ran tsohuwar lamba daya a wasan kwallon tennis din mata, Maria Sharapova ta dawo fagen wasa a gasar Malllorca Open mako mai zuwa, bayan share fiye da watanni 3 tana jinyar rauni.

Maria Sharapova yayin gasar Madrid Open a shekarar 2017
Maria Sharapova yayin gasar Madrid Open a shekarar 2017 REUTERS/Sergio Perez
Talla

Sharapova, ‘yar shekara 32, wacce sau biyar tana lashe babban kofin gasar tennis na Grand Slam, ta fara jinya ne tun a watan Fabrairu, bayan aikin tiyata da aka mata a kafadar da tun a shekarar 2008 ta fara mata ciwo.

Sharapova tana ta fadi - tashi na dawowa karsashinta ne tun bayan da aka kakaba mata horon dakatarwa sakamakon kama ta da laifin shan abubuwa masu kara kuzari, dakatarwar da ta kawo karshe a shekarar 2017.

A watan Janairu ne aka wa Sharapova ganin karshe a fagen wasa, yayin gasar St Petersburg Open, inda ta sha kashi a hannun Ashleigh Barty.

A ranar 17 ga wannan watan ne za a fara wannan gasa ta Mallorca Open, wanda ta kan ciyawa ce, inda Sharapova za ta hadu da gwarzuwar gasar Wimbledon Open, Angelique Keber, da ma tshuwar lamba daya a duniya Victoria Azarenka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.