Isa ga babban shafi
Faransa

Shugabannin Turai sun hadu a bikin cika shekaru 75 da fatattakar sojin Nazi a Faransa

A kwana a tashi yau shekaru 75 kenan cur, da sojoji dubu 150 da suka hada da na sama, na ruwa da na kasa, suka kaddamar da farmaki daga gabar ruwan Normandie, domin kwato Faransa daga hannun sojojin Jamus, lamarin da ya kasance silar murkushe ‘yan Nazi tare da kawo karshen Yakin Duniya na Biyu.

Bikin cika shekaru 75 da fatattakar sojin Nazi a Faransa
Bikin cika shekaru 75 da fatattakar sojin Nazi a Faransa REUTERS/Carlos Barria
Talla

Duk da cewa ranar 6 ga watan yunin shekara ta 1944 ne aka kaddamar da wannan farmaki, to amma tun a jiya laraba ne aka fara gudanar da bukukuwan tunawa da ranar.

Shugabannin duniya, ciki har da shugaba Donald Trump,da takwaransa na Faransa Emanuel Macron sun hadu a gabar ruwan Normandy a yau Alhamis, wurin da shekaru 75 da suka wuce dakarun kawance suka hadu don fatattakar mayakan Nazi daga Faransa.

A daidai lokacin da ake ci gaba da samun rashin jituwa tsakanin kasashe, shugabannin duniya zasu so su nuna hadin kan da ke tsakaninsu, yayin da suke haduwa a rana ta biyu don jinjina wa jaruntar sojojin da suka yunkuro daga gabar ruwan Normandy a ranar 6 ga watan Yunin shekarar 1944.

Tun da farko shugaba Macron da Firaministar Birtaniya Theresa May hadu don kaddamar da wani ginin Birtaniya na tunawa da mazan da suka sha fama a Ver – Sur – Mer, kuma daga bisani Macron da Trump zasu yi wata tattaunawar sirri.

Dubun dubatan Faransawa ne, da ma baki daga kasashen waje suka hallara a gabar ruwan Normandy don wannan bikin tunawa da mazan jiyan, tare da karrama wadanda suka shaidi yakin.

A wata muhimmiyar sanarwar hadin gwiwa, shugabannin kasashe 16 da suka kasasance a bikin da ya gudana a Portsmouth na Birtaniya, ciki har da shugaba Trump na Amurka sun sha alwashin tabbatar da cewa ba a sake samun aukuwar yaki irin yakin duniya na 2 ba.

Sai dai shugaban Rasha Vladimir Putin bai samu gayyatar halartar ko da daya daga cikin bukukuwan ba, lamarin da ke nuni da cewa dangata ta yi tsami tsakaninsa da shugabannin Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.