Faransa
Ana farautar mutumin da ya kai hari a Lyon na Faransa
Jami’an ‘yan sandan Faransa na farautar wanda ake zargi da hannu a wani harin bam da ya tashi a gefen titin birnin Lyon, inda sama da mutane 10 suka jikkata.
Wallafawa ranar:
Talla
Wannan na zuwa ne kwanaki biyu gabanin gudanar da zaben ‘Yan Majalisun Dokokin Kungiyar Tarayyar Turai a kasar.
Shugaban kasar, Emmanuel Macron ya bayyana fashewar bam din a matsayin hari, yayinda ya tura Ministan Cikin Gida zuwa can birnin Lyon.
Ana zargin wani matashi da kai wannan harin bayan hoton jami’an tsaro ya nuna shi yana kai-kawo akan kekensa gabanin fashewar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu