Isa ga babban shafi
Faransa

Harin bam ya jikkata mutane a Faransa

Rahotanni daga Faransa sun ce an samu fashewar wani abu da ake zaton bam ne a gefen titin birnin Lyon wanda ya yi sanadiyar jikkata mutane 8.

Wurin da aka samu tashin bam a birnin Lyon na Faransa
Wurin da aka samu tashin bam a birnin Lyon na Faransa Préfet de région Auvergne-Rhône-Alpes et du Rhône
Talla

Ya zuwa yanzu babu cikakken bayani kan fashewar, amma masu shigar da kara na gwamnati na zargin cewa, wani kunshin bam ne aka ajiye.

Tuni aka kwashe jama’a daga wurin da aka samu wannan hadarin kamar yadda ‘yan jaridun AFP suka rawaito.

Jami’an ‘yan sanda sun ce, wadanda suka samu raunin basa fuskantar barazanar rasa rayukansu.

A wata hira da aka watsa kai tsaye ta dandalin sada zumunta na Facebook, shugaban kasar, Emmanuel Macron ya bayyana fashewar a matsayin hari kuma babu wanda ya rasa ransa kawo yanzu a cewarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.