Isa ga babban shafi
Tarayyar turai

Masu tsattsauran ra'ayi ka iya samun tagomashi a zaben Turai

A yayinda aka fara gudanar da zaben Majalisar Dokokin Kasashen Turai, hankula sun karkata kan Birtaniya da Netherlands da ke kada kuri’unsu a yau, inda za su fayyace girmar karbuwar masu tsattsauran ra’ayi a nahiyar Turai.

Masu tsattsauran ra'ayi ka iya samun tagomashi a zaben Turai
Masu tsattsauran ra'ayi ka iya samun tagomashi a zaben Turai RFI Estudio Gráfico
Talla

Sama da mutane miliyan 400 daga jumullar kasashen Turai 28 za su kada kuri’u, inda za su zabi ‘yan Majalisar Dokokin Nahiyar 751 zuwa nan da ranar Lahadi, wato lokacin da za a kammala zaben tare da sanar da sakamako.

A yau ne Birtaniya da Netherland ke kada nasu kuri’un, yayinda a gobe Jumma’a kasashen Ireland da Jamhuriyar Czech za su kada nasu, inda kuma akasarin kasashen Turai za su halarci rumfunan zabe a ranar Lahadi mau zuwa, wato ranar karshe na zaben.

An bude rumfunan zabe da misalin karfe 5 :30 na safe agogon GMT a Netherlands, kuma jam’iyyar FvD da ke kyamar baki ce ke fafatawa da jam’iyyar VDD ta Firaminista Mark Rutte wadda ta bukaci magoya bayanta da su kayar da masu tsattsauran ra’ayi.

A can Birtaniya kuwa, masu tsattsauriyar akida sun lashi takobin haifar da rudanin siyasa da zai girgiza shugababcin Majalisar Dokokin Turai da ke birnin Brussels.

Ana ganin watakila masu tsattsauran ra’ayin kishin Turai su samu tagomashi a zaben na wannan karo, musamman idan aka yi la’akari da wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da ke nuna cewa, jam’iyyar Marine Le Pen mai tsattsauran ra’ayi a Faransa, ta sha gaban jam’iyyar shugaba Emmanuel Macron, kuma haka lamarin yake a Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.