An fara zaben EU bisa tsoron rinjayen masu tsattsauran ra'ayi
Jam'iyyun da ke kyamar baki a nahiyar Turai na kokarin bayar da mamaki a zaben 'yan Majalisun Tarayyar Turai da za’a fara yau a nahiyar baki daya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yanzu haka dai a faro zaben ne daga kasashen Birtaniya da Netherlands, kafin sauran kasashen su yi amfani da sauran kwanakin don kada tasu kuri'ar.
Fiye da mutane miliyan 400 ake saran su kada kuri'a a zaben na Majalisar Tarayyar Turai inda za su zabi Yan Majalisu 751 a kasashen nahiyar 28.
Shugabannin kasashen Nahiyar dai Galibi Emmanuel Macron na Faransa da Angela Merkel ta Jamus sun ja hankalin magoya bayansu don kaucewa kin fitowa kada kuri'a a zaben mai matukar muhimmanci, wanda suka ce rashin fitowar jama'a ne ka iya jefa mulkin hannun masu tsattsauran ra'ayi.
A bangare guda Kasar Birtaniya da ke kokarin ficewa daga kungiyar ta EU, Majalisar Turai ta tilasta mata shiga zaben ne bayan rashin amincewar Majalisar kasar da yarjejeniyar da Theresa May ta kulla da EU kan ficewar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu