Isa ga babban shafi
Faransa-LAFIYA

Kotu ta yi umarnin bai wa wani majinyaci a Faransa damar mutuwa

Dai dai lokacin da likitoci a Faransa suka fara aikin kwance na’urorin bayar da tallafin rayuwa ga Vincent Lambert da ke kwance tsawon shekaru 10 a asibiti, kotu ta yi watsi da karar da iyalansa su ka daukaka don ganin an ci gaba da bashi damar rayuwa.

Iyalan majinyacin Vincent Lambert da kotu ta yi watsi da daukaka kararsu kan bai wa majinyacin damar rayuwa
Iyalan majinyacin Vincent Lambert da kotu ta yi watsi da daukaka kararsu kan bai wa majinyacin damar rayuwa FRANCOIS NASCIMBENI / AFP
Talla

Tun bayan samun hadarin mota a shekarar 2008 lokacin ya na da shekaru 32 a duniya, Vincent Lambert wanda jami’in lafiya ne, ya gamu da matsalar kwakwalwa baya ga shanyewar ilahirin sassan jikinsa matakin da ya tilasta likitoci a asibitin birnin Reims ba shi tallafin rayuwa ta hanyar amfani da na'urori.

Sai dai a shekarar 2011 likitocin suka tabbatar da Vincent ba ya da sauran rayuwa a gaba, inda kuma a shekarar 2013 suka bukaci kwance na’urorin da ke tallafa masa ci gaba da rayuwa, bisa bukatar matarsa, matakin da ya ci karo da bukatar mahaifansa wadanda su ka nemi ci gaba da bashi damar rayuwa.

Haka zalika a shekarar 2014 likitocin suka sake mika bukatar kwance naurorin tallafawa Lambert bisa kafa hujja da dokar kasar da ta bayar da damar saukakawa majinyaci mutuwa matukar ya gaza samun lafiya, sai dai tuni iyayen suka sake daukaka kara inda kotu ta yi umarnin ci gaba da bashi kula.

Sai dai kuma bayan gudanar da wani bincike da ya nuna Lambert ba zai taba warkewa ba, wata kotu a Strassbourg ta yi umarnin ba shi damar mutuwa.

Ko a watan Janairun da ya gabata ma, makamancin abin da ya wakana kenan inda kotuna a matakai daban daban suka goyi bayan baiwa majinyacin damar mutuwa.

Sai dai iyalan Vincent Lanbert ba su hakura ba, don kuwa bayan da asibitin ya sanar da matakin kwance nau’rorin bai wa Lambart rayuwa, a shekaran jiya Asabar sun mika kokensu gaban shugaba Emmanuel Macron don ya dakatar da asibitin daga katse na’uroin, yayinda suka sake daukaka kara amma kotu ta yi watsi da bukatarsu a yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.