Isa ga babban shafi
Birtaniya

Brexit: May ta soma yunkurin karshe kan sabuwar yarjejeniya

Fira Ministar Birtaniya ta soma yunkurin karshe na gabatar da sabuwar yarjejeniyar ficewa daga kungiyar Turai ga ‘yan majalisun kasar domin ganin sun amince da ita.

Fira ministar Birtaniya Theresa May.
Fira ministar Birtaniya Theresa May. Jack Taylor / POOL / AFP
Talla

Yayin da take bayyana aniyar sake gabatar da yarjejeniyar ficewa daga kungiyar kasashen Turan, Fira minista Theresa May tace har yanzu tana da yakinin samun goyan bayan Karin Yan Majalisu da zasu amince da shirin ta.

Sau uku yan majalisun na sa kafa suna shure shirye shiryen da Fira minista May ta gabatar musu, matakin da ya tilasta jinkirta ficewar kasar daga ranar 29 ga watan Maris zuwa 12 ga watan Afrilu sai kuma zuwa 31 ga watan Oktoba mai zuwa.

Masu sa ido kan siyasar Birtniya sun ce tuni karfin ikon Fira ministar yayi rauni, ganin yadda take ta shan kaye a zauren Majalisar, kuma hakan na iya haifar da kalubalantar shugabancin ta a Jam’iyyar su ta masu ra’ayin rikau, da zaran an kamala daukar matsayi kan yarjejeniyar.

A karshen makon da ya gabata, Jam’iyyar Labour ta sanar da janyewa daga duk wata tattaunawar da ta shafi shirin ficewa daga kungiyar Turai, da kuma jaddada aniyar ta na kada kuri’ar kin amincewa da sabuwar yarjejeniyar, kamar yadda shugaban ta Jeremy Corbyn ya bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.