Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta yi ikirarin samun 'yan yawon bude ido miliyan 90 a bana

Wata kididdiga da gwamnatin Faransa ta fiar ta nuna cewa kasar ta karbi bakoncin baki ‘yan yawan bude ido akalla miliyan 90 cikin shekarar da ta gabata, dukkuwa da zanga-zangar adawa da gwamanti da masu yaluwar riga ke ci gaba da yi a kasar, wadda ta haddasa nakasu ga tattalin arzikinta.

Guda cikin bakin ruwan da ke kayatar da 'yan yawon bude ido a Faransa
Guda cikin bakin ruwan da ke kayatar da 'yan yawon bude ido a Faransa AFP
Talla

Gwamnatin ta Faransa ta bayyana cewa, hasashen da aka yi na fuskantar karancin masu ziyartar kasar bai tabbata ba, inda har yanzu Faransar ke a matsayin sahun gaba wajen karbar yawan ‘yan yawon bude ido a Nahiyar Turai.

Sanarwar gwamnatin ta ce adadin maziyartan na ta ya karu da akalla kashi 3 idan aka kwatanta da na 2017 inda ta ce ta na fatan yawansu yak ai miliyan 100 a shekara mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.