Isa ga babban shafi
Turai

Shugaban Faransa ya gana da yan kasar da yan bindiga suka yi garkuwa da su

Faransawa nan da wasu yan bindiga suka yi awon gaba da su a cikin dajin yawon bude ido na Pendjari dake Jamhuriyar Benin daf da kan iyaka da kasar Burkina Faso sun sauka Faransa.Shugaban kasar Emmanuel Macron da kan sa ne ya tarbi Faransawa da saukar su daga cikin jirgi a filin tashi da sauka jirgin sama na Villacoublay dake kusa da Paris.

Mutanen da yan bindiga suka yi garkuwa da su a Burkina Faso
Mutanen da yan bindiga suka yi garkuwa da su a Burkina Faso REUTERS/Anne Mimault
Talla

Da saukar su ,Ministan harakokin wajen Faransa Jean Yves Ledrian ya roki yan kasar da suk kaucewa zuwa yankuna dake tattare da hatsari ,ya gargade su da cewa Faransawa na daga cikin mutanen da yan ta’ada suke nema a yankin Sahel.

Daya daga cikin Faransawan mai sunan Laurent Lassimouillas ya bayyana godiyar sa zuwa Faransa da sauren kasashe da suka taimaka aka ceto su.

00:32

Daya daga cikin Faransawa da aka ceto daga hannun yan ta'ada a Burkina Faso

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.