Isa ga babban shafi
Faransa

An karrama 'yan jaridun Faransa da aka hallaka a bakin aiki

Yau Juma’a aka kaddamar da wani dandali a birnin Paris na kasar Faransa dauke da sunan ‘yan jaridun kasar uku da aka kashe a nahiyar Afirka yayin gudanar da aikin su.

Yan Jaridun Gidan Rediyon Faransa da aka hallaka a bakin aiki, Ghislaine Dupont da Claude Verlon da gwamnatin Faransa ta karrama.
Yan Jaridun Gidan Rediyon Faransa da aka hallaka a bakin aiki, Ghislaine Dupont da Claude Verlon da gwamnatin Faransa ta karrama. RFI
Talla

A dalilin ‘yan Jaridun ne Majalisar Dinkin Duniya ta ware 3 ga watan Mayu a matsayin ranar ‘yan jaridu ta duniya.

Yayin bukin kaddamar da dandalin a gaban dimbin jama’a, magajin garin birnin Paris na 2, Jacques Boutault, ya ce ba za a taba mantawa da sadaukarwar ‘ya jaridun ba, wato Ghislaine Dupont da Claude Verlon, sai kuma Camille Lepage.

Ghislane Dupont da Claude Verlon dai ‘yan jaridu ne da ke aiki da sashin Faransanci na Radio France International RFI, wadanda aka kashe a kasar Mali yayin da suke kan gudanar da aikinsu, shi kuma Camille Lepage mai daukar hoto ne da aka kashe a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya a shekarar 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.