Isa ga babban shafi
Turai

Gobara ta lakume cocin Notre Dame mafi tarihi a Faransa

Wata gagarumar gobara ta mamaye katafaren ginin babban cocin Notre-Dame dake birnin Paris na kasar Faransa, kuma yanzu haka jami’an kashe gobara na can suna kokarin kashe wutar. Bayan da gobara ta tashi a Coci mafi tarihi da aka sani da Notre Dame dake Paris a kasar Faransa,Shugaban kasar ya jinkirta jawabin sa dangane da sabon shiri da zai haifar da sauye sauyen manufofin gwamnatin sa.

Gobara ta mamaye katafaren ginin babban cocin Notre-Dame dake birnin Paris
Gobara ta mamaye katafaren ginin babban cocin Notre-Dame dake birnin Paris ©Patrick ANIDJAR/AFP
Talla

Cocin Notre-Dame da hukumar kula da kayan tarihi ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanya shi cikin wuraren tarihi na duniya, na daya daga cikin wuraren dake samun baki kusan milyan 13 daga sassan duniya dake kai masa ziyara a kowacce shekara.

Shugaba Emmanuel Macron ya bayyana kaduwar sa da gobarar wanda ya bayyana na a matsayin abin takaici, inda yake cewa kamar kowanne dan Faransa yana cike da bakin ciki kan lamarin.

Tuni shugaban ya bayyana dakatar da jawabin da ya shirya gabatarwa al’ummar kasar kan sauya wasu manufofin gwamnatin sa.

Alkaluman da hukumomin kasar suka bayar sun nuna cewa, wutar ta lashe fadin rufin cocin dake dauke da dimbin tarihi.

Tuni Shugabanin Kasashen Duniya suka fara mayar da martani kan gobarar wadda ta yiwa ginin cocin illa.

Cikin wadanda suka bayyana takaicin su harda Shugaban Amurka Donald Trump da Shugabar gwamnatin Jamus ,Angela Merkel da Magajin garin London Sadiq Khan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.