Isa ga babban shafi
Brexit

May ta bukaci sake jinkirta ficewar kasar daga EU

Firaministar Birtaniya, Theresa May ta bukaci Kungiyar Tarayyar Turai da ta jinkirta ficewar kasar daga nahiyar har zuwa ranar 30 ga watan Yuni mai zuwa.

Firaministar Birtaniya Theresa May
Firaministar Birtaniya Theresa May REUTERS/Peter Nicholls
Talla

Tun da fari dai, an shirya cewa, Birtaniya za ta raba gari da Turai a ranar 12 ga watan nan na Afrilu, sai dai har yanzu Majalisar Dokokin Kasar bata amince da yarjejeniyar ficewar ba a wannan rana.

Firaministar ta bayyana cewa, muddin Majalisar ta amince da yarjejeniyar a kan lokaci, to kasar za ta iya ficewa baki daya gabanin zaben Majalisar Dokokin Tarayyar Turai da za a gudanar a ranar 23 ga watan Mayu.

Sai dai a cewarta, Birtaniya za ta gabatar da nata ‘yan takarar a zaben na ‘yan Majalisun Dokokin Turan saboda watakila a gaza cimma wata matsaya kan ficewar.

A bangare guda, Kungiyar Tarayyar Turai ta bayar da shawarar cewa, watakila zai fi dacewa kasar ta Birtaniya ta jinkirta ficewarta har nan da shekara guda.

Bangarorin biyu za su sake wani zama a birnin Brussels a ranar Laraba mai zuwa duk dai kan batun ficewar, amma masharhanta na cewa, bisa dukkan alamu, Uwargida Theresa May ba za ta samu nasara ba a ganawar da mahukuntan na Turan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.