Isa ga babban shafi
Birtaniya

May ta gana da 'yan adawa kan ficewar Birtaniya daga EU

Firaministar Birtaniya, Theresa May ta gana da shugaban ‘yan adawar kasar da zummar shawo kansa dangane da fafutukarta ta ficewa daga gungun kasashen Turai cikin mutunci.

Firaministar Birtaniya Theresa May
Firaministar Birtaniya Theresa May REUTERS/Peter Nicholls
Talla

Uwargida Theresa May ta nemi goyon bayan shugaban ‘yan adawa, Jeremy Corbyn a wata ganawar ba-za-ta da za ta fayyace makomar gwamnatinta.

Mai magana da yawun fadar gwamnatin May, ya ce, tattaunawar da aka yi tsakanin bangarorin biyu mai ma’ana ce, domin kuwa kowanne bangare ya yi sako-sako tare da nuna aniyar dinke dambarwar ficewar.

A karo na uku, Majalisar Dokokin kasar ke fatali da yarjejeniyar da May ta cimma da kasashen Turai 27, yayinda hakurin mahukuntan na Turai ke gab da karewa, ganin cewa wa’adin da suka ba ta na ficewa daga kungiyar nan da 12 ga watan Afrilu ba tare da cimma matsaya ba na gab da cika.

Firaministar ta ce, za ta sake neman wani jinkirin ficewar a taron da zai gudana tsakaninta da shugabannin kasashen na Turai a Brussels a ranar 10 ga watan nan na Aprilu.

Uwargida May ta kara da cewa, a yanzu tana da muradin sassauta ka’idojin da ta gabatar a can baya, sannan kuma za ta saurari kudurorin ci gaba da huldar kasuwanci da nahiyar Turai bayan kammala ficewar baki daya.

Sai dai bayanai na nuni da cewa, da dama daga cikin mambobin jam’iyyarta ta Conservative ba sa goyon bayan wannan matakin da ta dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.