Isa ga babban shafi
Faransa

Macron na neman hadin kan 'yan siyasar Faransa

Shugaban Faransa Manuel Macron, na neman janyo jami’iyyu masu rajin kare muhalli cikin batun zaben Majalisar Tarayyar Turai don yin wani hadin gwiwa da su  bayan zaben na watan Mayu.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Eva Plevier
Talla

Wani wanda ke cikin ‘yan takaran da shugaba Macron ke goya wa baya, Pascal Canfin ya ce, za su jagoranci wani kokarin hadin gwiwa da zai bai wa jam’iyyun masu fafutukar kare muhalli damar shiga a dama da su.

Shugaba Macron yana so ne ya wargaza mamayar da jam’iyyu masu ra’ayin mazan jiya na EPP da S & D suka yi ne a Majalisar Tarayyar Turai, kamar yadda ya yi wa manyan jam’iyyu a zaben shekarar 2017.

Binciken da aka gudanar kan muradan masu zabe na nuni da cewa jamiyyun EPP da SD ba za su iya samun gagarumin rinjaye ba, lamarin da ake ganin zai tsayar da ‘yan tsaka-tsakin da Macron ke fatan hada kansu a matsayin masu fada a ji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.