Isa ga babban shafi
Faransa

Gwamnatin Faransa ta haramta zanga-zanga a wasu birane

Gwamnatin Faransa ta girke dubban ‘Yan Sanda a birnin Paris da sauran manyan biranen kasar, domin dakile maimaituwar tashin hankalin da ya faru yayin zanga-zangar masu rigunan dorawa ta makon jiya.

'Yan sandan Faransa a gaban wani shagon saida kayayyaki da ke yankin Champs-Elysees, da masu zanga-zanga suka kunnawa wuta a birnin Paris, yayin zanga-zangar makon da ya gabata.
'Yan sandan Faransa a gaban wani shagon saida kayayyaki da ke yankin Champs-Elysees, da masu zanga-zanga suka kunnawa wuta a birnin Paris, yayin zanga-zangar makon da ya gabata. AFP/File/Zakaria ABDELKAFI
Talla

A makon da ya gabata wani gungu daga cikin masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Macron ya tayarda bore, lamarin da ya kai ga fasa manyan shaguna, da kone dukiya mai tarin yawa ciki har da wani banki a birnin Paris.

Yau Asabar dai, makarantu, bankuna da sauran manyan shagunan kasuwanci da ke birnin na Paris sun kasance a rufe, zalika inda aka kara da baiwa ilahirin gilasan tagogin gine-gine tagoginsu tsaro na da katako don gudun yi musu rotse da duwatsu.

A biranen da suka hada da Bordeaux, Dijon, Rennes, Tolouse da Nice kuwa, hukumomin tsaron kasar ta Faransa sun haramta dukkan wani nau’i na gudanar da zanga-zanga, la’akari da tashin hankalin da aka samu a makon da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.