Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

EU za ta iya amincewa da jinkirta ficewar Birtaniya daga cikinta - Tusk

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai, Donald Tusk ya ce mai yiwuwa shugabannin Turai su amince da jinkirta ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar kasashen Turai EU.

Shugaban Majalisar Zartarwar kungiyar tarayyar Turai Donald Tusk tare da Fira Ministan Birtaniya Theresa May.
Shugaban Majalisar Zartarwar kungiyar tarayyar Turai Donald Tusk tare da Fira Ministan Birtaniya Theresa May. Francisco Seco/AFP/Getty Images
Talla

Tusk ya bayyana haka ne yayinda Fira Minista Birtaniya Theresa May ke gaf da mika kokon barar neman karin lokacin kammala ficewa daga karkashin EU, ga takwarorinta na Turai.

Cikin tsokacin da takwarorin Birtaniya suka yi gangane da bukatar ta Birtaniya, Faransa, ta bakin ministan harkokin wajenta, Jean yves Le Drian ta ce ba mamaki ta ki goyon bayan tsawaita wa’adin barin kungiyar ga Birtaniya har sai ta amince da wasu sharrudda, da suka hada da neman kada ta shiga zabukan Majalisar kungiyar kasashen na tarayyar Turai da ke tafe ranar daga 23 zuwa 26 ga watan Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.