Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta yi amfani da sojoji don murkushe masu zanga-zanga

Gwamnatin Faransa ta ce za ta girke tarin dakarun Soji don sanya idanu kan masu zanga-zangar yaluwar riga a kasar, matakin da ke da nufin kaucewa, arangamar da aka fuskanta makon jiya tsakanin masu zanga-zangar ta mako-mako da jami’an tsaro wadda ta kai ga barnata kayakin al’umma.

Yayin zanga-zangar makon jiya dai gwamnatin Faransa da kanta ta amince da gazawar jami'an tsaronta
Yayin zanga-zangar makon jiya dai gwamnatin Faransa da kanta ta amince da gazawar jami'an tsaronta ©REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Mai magana da yawun gwamnatin Faransa Benjamin Griveaux ya shaidawa manema labarai cewa dakarun sojin za su yi aikin kula da manyan tituna filayen jiragen sama da na kasa da wuraren ibada da ma sauran kadarorin gwamnatin da ke girke a biranen da zanga-zangar ke gudana.

A cewar kakakin gwamnatin na Faransa, wannan sabuwar dabara za ta bai wa jami’an ‘yan sanda cikakkiyar damar kula da masu yin gangamin a ranar Asabar, ta hanyar tabbatar da doka da Oda.

Tuni dai wasu kungiyoyin ‘yan sanda suka fara caccakar matakin gwamnatin na Faransa bisa cewa sojoji basu da hurumin kula da masu zanga-zangar.

A bangare guda wata majiyar Fadar shugaban kasa ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransar cewa, akwai shirye-shiryen tube wasu manyan jami’an ‘yan sanda 2 gabanin zanga-zangar.

Baya ga sabbin matakan tsaron, fadar gwamnatin Faransar ta Elysee ta ce akwai yiwuwar haramta gudanar da zanga-zanga a yankunan da ke gab da fadar dama wasu muhimman yankuna na birnin Pari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.