Isa ga babban shafi
Turai

Kotu a Australia ta yanke hukuncin daurin zuwa Cardinal George Pell

Wata Kotu a Australia ta yanke hukuncin daurin shekaru 6 a gidan yari kan wani tsohon babban limamin coci, Cardinal George Pell da aka samu da laifin lalata da wasu yara biyu dake aiki a cocin.

Paparoma Francis cikin juyayi yan lokuta bayan da kotu ta yanke hukunci
Paparoma Francis cikin juyayi yan lokuta bayan da kotu ta yanke hukunci Photo: Vincenzo Pinto/Pool/AFP
Talla

Cardinal Pell wanda shine tsohon mutumi na uku a jerin shugabannin mabiya darikar Katolika dake fadar Vatican, wanda ke kula da baitulmali, kana kuma ya taimaka wajen zabo fafaroma guda biyu, ya aikata laifin ne tsakanin shekarar 1996 zuwa 1997.

Alkalin kotun, Peter Kidd ya bayyana halayen Cardinal Pell mai shekaru 77 a matsayin abin takaici da kuma Allah wadai saboda kimar sa da mukamin da ya rike.

Cardinal Pell mai shekaru 77 yace zai daukaka kara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.