Isa ga babban shafi
Venezuela

Magoya bayan Maduro da Guaido sun sabunta zanga-zanga

Dubban ‘yan Venezuela sun sake fita zanga-zanga a babban birnin kasar Caracas, domin amsa kiran shugaba Nicolas Maduro da kuma na Jagoran ‘yan adawa Juan Guaido da ya ayyana kansa a matsayin halastaccen shugaba.

Dubban masu zanga-zanga a Venezuela.
Dubban masu zanga-zanga a Venezuela. AFP Photo/Federico PARRA
Talla

Jagoran ‘yan adawa Juan Guaido, ya bukaci magoya bayansa da su sabunta aniyar kawo karshen gwamnatin Maduro, yayinda a nasa bangaren, shugaba Maduro ya bukaci, nasa magoya bayan su nunawa duniya cewa, har yanzu shi ne karbabben shugaba a garesu.

Sabuwar zanga-zangar kashi biyu, ta barke ne bayan da aka shiga rana ta uku da rasa wutar lantarki a mafi akasarin sassan kasar, lamarin da ya gurgunta ayyukan asibitoci inda marasa lafiya 13 suka rasa ransu.

Rashin wutar lantarkin ya kuma gurgunta hada-hadar masana’antu da kuma sauran ma’aikatun kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.