Isa ga babban shafi
Faransa

Ana zargin manyan mukarraban Macron da sharara karya

Zauren Majalisar Dattijan Faransa, ta bukaci bincikar wasu manyan mukarraban shugaba Emmanuel Macron, bayan da wani kwamitin majalisar ya gano cewa, manyan jami’an sun gaza wajen hukunta tsohon dogarin Macron, da aka samu da wasu jerin laifuka, wato Alexander Banella.

Alexandre Benalla tsohon dogarin shugaba Emmanuel Macron, yayin rantsuwa kafin kare kansa daga zargin laifuka a zauren majalisar dattijan Faransa.
Alexandre Benalla tsohon dogarin shugaba Emmanuel Macron, yayin rantsuwa kafin kare kansa daga zargin laifuka a zauren majalisar dattijan Faransa. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Manyan mukarraban shugaba Macron da Zauren majalisar dattijan ta Faransa ke zargi sun hada da shugaban ma’aikata Patrick Strzoda, sakataren gwamnati Alexis Kohler da kuma shugaban Jami’an tsaro Lionel Lavergne.

Majalisar ta zargi manyan jami’an gwamnatin ta Faransa da yin karya kan wasu shaidu da suka bada dangane da laifin cin zarafin farar hula da tsohon Dogarin shugaba Macron Alexender Banella yayi a watan Mayu na 2018.

Zalika an zargi manyan jami'an na shugaba Macron da bayar da shaidun karya, wajen kare laifin Benalla na amfani da fasfonsa wajen ayyukan diflomasiyya ba bisa ka’ida ba, duk da cewa yana da masaniyar an dakatar da shi daga aikinsa, sai dai gwamnati ta yi watsi da rahoton, wanda ta bayyana shi a matsayin mai cike da hujjojin bogi.

Tuni dai masu gabatar da kara na Faransa suka kaddamar da sabon bincike kan Benalla, bisa zarginsa da kokarin hana masu bincike gudanar da aikinsu ta hanyar boye shaidun gaskiya da kuma gabatar da na karya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.