Isa ga babban shafi
Spain

Sabon Firaministan Spain na fuskantar kalubale

Dubban ‘yan Spain dauke da Tutocin kasar sun amsa kiran fita zanga-zanga a birnin Madrid, bisa jagorancin jami’yyun kasar masu ra'ayin rikau da na sassauci.Zanga-zangar dai ta nuna adawa ce ga Firaministan Spain Pedro Sanchez, bisa shirinsa na ganawa da jagororin ‘yan awaren kasar don kulla kawance.

Zanga-zangar wadda manyan jam'iyyun kasar 3 suka kira, na zuwa lokacin da ya rage kwana guda a fara sauraron shari'ar jagororin 'yan awaren yankin Catalonia da suka jagoranci yunkurin ballewa
Zanga-zangar wadda manyan jam'iyyun kasar 3 suka kira, na zuwa lokacin da ya rage kwana guda a fara sauraron shari'ar jagororin 'yan awaren yankin Catalonia da suka jagoranci yunkurin ballewa 路透社
Talla

‘Yan sandan Spain sun ce akalla mutane dubu 45 ne suka halarci zanga-zangar a birnin Madrid a karkashin jagorancin jam'iyyun PP, Ciudadanos da Vox, yayinda ya rage kwanaki biyu, a fara sauraron shari'ar wasu manyan jagororin ‘yan awaren yankin Catalonia da ke neman ballewa daga kasar ta Spain.

Jam'iyyun dai sun fusata ne da kokarin sabon Firaministan na Spain Pedro Sanchez na tattaunawar sulhu da jam'iyyu masu goyon bayan ballewar yankin Catalonia daga kasar, wadanda ya ke neman goyon bayansu domin taimakawa wasu manufofinsa na samun amincewar majalisar dokokin kasar da suka fi rinjaye.

A watan Yunin bara Sanchez ya dare kujerar Firaministan Spain da taimakon jam'iyyun na PP, Ciudadanos da Vox, bayan da ‘yan majalisunsu suka kada kuri'ar yankan kauna ga gwamnatin tsohon Firaminista Mariano Rajoy.

Wata kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a ta nuna cewa muddin aka gudanar da babban zaben Spain a yanzu, to fa jam'iyyun uku ne za su lashe kujerun majalisar kasar da gagarumin rinjayen da zai ba su damar sauke Firaminista Sanchez.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.