Dubban 'yan Venezuela sun tsere zuwa Spain
Rahotanni daga Venezuela sun ce dubban ‘yan kasar sun tsere zuwa Spain, don gujewa rikicin siyasar da ke barazanar juyewa zuwa kazamin rikici, tsakanin shugaba Maduro da jagoran ‘yan adawa Juan Guaido da kasashen Turai ke marawa baya a matsayin shugaban rikon kwarya.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar kididdigar Spain ta ce a halin yanzu, ‘yan kasar Venezuela kimanin dubu 255 ne suka shiga kasar.
Sai dai wata majiya da kungiyar ‘yan Venezuela mazauna kasashen ketare ta ce yawan wadanda suka tsere zuwa Spain din zai iya kaiwa dubu 300, idan aka hada da wadanda suka ketara cikin kasar babu izni.
A halin da ake ciki Amurka ta mikawa kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya kudurin tilasta shigar da kayan agaji cikin Venezuela, wadana shugaba Maduro ya sha alwashin hanawa, sai kuma tilasta shirya sabon zaben shugaban kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu