A makon jiya dai adadin masu zanga-zangar da suka fita titunan kasar ta faransa bai gaza mutum dubu 58 da 600 ba, ko da dai masu zanga-zngar sun yi ikrarin cewa yawansu ya kai dubu 116.
Wani bangare na masu zanga-zangar dai sun nuna bukatar hadewa da kungiyoyin kwadagon kasar don neman biyan bukatarsu da saukaka matsin rayuwa, yayinda jagororin suka tsaya kan bakansu na ganin shugaba Emmanuel Macron ya yi murabus.