Isa ga babban shafi
Faransa

Gobara ta kashe mutane a birnin Paris

Akalla mutane 8 sun rasa rayukansu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani gini mai hawa takwas da ke birnin Paris na Faransa kamar yadda jami’an kashe gobarar suka tabbatar.

Gini mai hawa takwas da ya kama da wuta a birnin Paris na Faransa
Gini mai hawa takwas da ya kama da wuta a birnin Paris na Faransa B. Moser/Brigade des Sapeurs-Pompiers de Paris (BSPP) via REUTER
Talla

Kimanin mutane 30 da suka hada jami’an kashe gobarar shida suka samu rauni a ibtila’in na ranar Talata.

Tuni aka kwashe akalla mutane 50 daga wannan ginin, yayin da mai shigar da kara na Faransa ke cewa, da yiwuwar cewa, da gangan aka tayar da gobarar, kuma tuni jami’an ‘yan sanda suka tsare wata mata da ake zargi.

Rahotanni na cewa, an shawo kan wutar gobarar bayan kwashe tsawon sa’o'i biyar ana aikin kawar da ita, amma ana ganin watakila adadin wadanda suka mutu ya karu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.