Isa ga babban shafi
Faransa

'Yan sanda sun yi sanadin tsiyayewar idanun masu zanga-zanga

Wata kungiyar kare hakkin dan adam tare da kungiyar ‘yan kasuwar Faransa, sun shigar da karar ‘yan sandan kasar gaban kotu, inda suke neman ta haramtawa jami’an tsaron yin amfani da harsasan roba kan masu sanye da rigunan dorawa da ke zanga-zanga.

Jerome Rodrigues, Daya daga cikin masu sanye da rigunan dorawa da ke zanga-zangar adawa da gwamnatin Faransa. Jerome Rodrigues, daya ne daga cikin wadanda suka samu rauni a idanunsu a dalilin arrangama tsakaninsu da 'yan sanda.
Jerome Rodrigues, Daya daga cikin masu sanye da rigunan dorawa da ke zanga-zangar adawa da gwamnatin Faransa. Jerome Rodrigues, daya ne daga cikin wadanda suka samu rauni a idanunsu a dalilin arrangama tsakaninsu da 'yan sanda. AFP/Zakaria ABDELKAFI
Talla

Kafin daukar matakin shigar da karar zuwa babbar kotun, sai da masu raji kare hakki na dan adam suka fara garzayawa wata karamar kotu, amma ta yi watsi da bukatar tasu.

Kungiyoyin sun bukaci haramtawa ‘yan sandan na Faransa amfani da harsasan robar ka masu zanga-zangar ne, saboda yawan wadanda jami’an tsaron suka raunata, yayin kokarin kawo karshen boren da suke yi a sassan kasar.

A cewar kungiyoyin, suna da hotunan mutane 13 da suka samu raunuka a idanunsu daga cikin jimillar masu zanga-zanga 20 da bincikensu ya tabbatar cewa harbinsu da harsasan robar masu tsawon inci daya da rabi ne ya yi sanadin tsiyayewar idanunsu akalla guda.

Sai dai gwamatin Faransa ta kare kanta da cewa, Tilas ce ta sanya ‘yan sandan kasar yin amfani da harsasan robar, domin hana wasu daga cikin masu zanga-zangar haddasa mummunan tashin hakali da suka yi yunkuri yi.

Ranar 17 ga watan Nuwamban bara, masu sanye da rigunan dorawa suka kaddamar da zanga-zangar adawa da manufofin tattalin arziki, na gwamnatin Emmanuel Macron, bayan da ta kara farashin albarkatun mai. Zuwa yanzu kuma masu zanga-zangar, sun shafe makwanni 10 suna fita a kowace rana ta Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.