Isa ga babban shafi
Mexico

Rayuka sama da 70 sun salwanta a Mexico

Hukumomin kasar Mexico sun ce, adadin mutanen da suka mutu sakamakon gobarar da ta tashi lokacin dibar mai a wani bututu da ya fashe ya karu daga 66 zuwa 73.

Sojin kasar Mexico yayin sintiri a yankin Tlahuelilpan da aka samu fashewar butun mai da ya hallaka mutane 66.
Sojin kasar Mexico yayin sintiri a yankin Tlahuelilpan da aka samu fashewar butun mai da ya hallaka mutane 66. AP
Talla

Gwamnan Jihar Hidalgo, Omar Fayad, yace adadin ya karu ne bayan gano wasu karin gawarwaki 5, a gobarar da wasu mutane akalla 74 suka jikkata.

Wani faifan bidiyon da aka nada a wajen hadarin, ya nuna yadda mutane ke ci da wuta, yayin da wasu na gudu suna bukatar taimako.

Tuni shugaban kasa Andres Manual Lopez Obrador ya tafi yankin domin ganewa idan sa halin da ake ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.