Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Alhaji Sirajo Labbo Jankado Musawa kan matakin Macron na fara muhawarar watanni 3 da masu zanga-zanga

Wallafawa ranar:

A kokarin kawo karshen zanga-zanga masu ruwan dorawar riga da ake kira da Yellow Vests a Faransa wadda ta shiga mako na goma, shugaban kasar Emmanuel Macron ya yi tayin fara muhawarar tsawon watanni uku don jin ra'ayoyin mutane.Macron ya fadi a jawabi ga mutan kasar cewa ba zai kauce daga manufofin yakin neman zaben sa ba. Shin ko matakan da Macron ya gabatar zai kawo karshen zanga-zangar. Tambayar ke nan da Garba Aliyu Zaria ya yi wa Alhaji Sirajo Labbo Jankado Musawa wanda shi ne Sarkin Hausawan Turai da ke zaune a Paris.

Mako na 10 kenan da dubban jama'ar ke gudanar da zanga-zanga a kasar ta Faransa kan tsadar rayuwar da suka ce gwamnati ta kakaba musu.
Mako na 10 kenan da dubban jama'ar ke gudanar da zanga-zanga a kasar ta Faransa kan tsadar rayuwar da suka ce gwamnati ta kakaba musu. AFP/Geoffroy van der Hasselt
Talla

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.