Isa ga babban shafi
Faransa

Shugabar hukumar kare manufofin Macron ta yi murabus

Shugabar hukumar shirya muhawara kan kare manufofin gwamnatin Faransa, dangane da al’amuran tattalin arziki, muhalli da kuma Haraji, Chantal Jouanno ta ajiye mukaminta.

Chantal Jouanno, tsohuwar Ministar wasannin Faransa, kuma tsohuwar shugabar hukumar shirya muhawara kan kare manufofin gwamnatin Faransa, dangane da al’amuran tattalin arziki.
Chantal Jouanno, tsohuwar Ministar wasannin Faransa, kuma tsohuwar shugabar hukumar shirya muhawara kan kare manufofin gwamnatin Faransa, dangane da al’amuran tattalin arziki. REUTERS/Mike Hutchings/File Photo
Talla

Jouanno ta dauki matakin ne, yayin da ya rage mako guda a kaddamar da muhawara kan sabbin manufofin shugaba Macron a makon gobe.

Yayin sanar da matakin nata na yin murabus, Chantal Jouanno, ta ce ajiye mukaminta ya zama tilas, la’akari da cewa, ba ta da tabbas, kan samun nasarar gwamnati wajen gamsar da Faransawa su amince da manufofinta na karfafa tattalin arzikinsu.

Sai dai a gefe guda, ana alakanta murabus din na Jouanno, da rahoton da wata mujalla ta wallafa da ke cewa, tana karbar makudan kudin da yawansu ya kai dala dubu 16,800, a matsayin albashin shugabantar hukumar shirya muhawarar kan manufofin gwamnatin ta Faransa.

A makon gobe za’a soma muhawara kan sabbin manufofin shugaba Macron a ilahirin manyan dakunan taron da ke biranen Faransa, da kuma a shafukan sadarwar intanet na zamani, muhawarar kuma za ta maida hankali kan batutuwan da suka shafi Muhalli, haraji, hakkokin ‘yan kasa da kuma tsarin dimokaradiyya.

Muhawarar dai bangare ne daga yunkurin shugaba Macron na maido da karbuwarsa ga Faransawa, bayan boren da shafe makwanni yana fuskanta, na zanga-zangar masu rigunan dorawa, kan manufofinsa na tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.