Isa ga babban shafi
Faransa

Zanga-zangar masu rigunan dorawa ta sake kankama a Faransa

Zanga-zangar masu rigunan dorawa da ke kin jinin gwamnati a Faransa ta sake kankama a wannan karshen mako, bayan da dubban masu zanga-zangar sukai fitar dango a Paris da sauran sassan kasar.

Masu zanga-zangar a Faransa, yayin arrangama da 'yan sanda a Champs-Elysees da ke birnin Paris.
Masu zanga-zangar a Faransa, yayin arrangama da 'yan sanda a Champs-Elysees da ke birnin Paris. AFP
Talla

Ma’aikatar cikin gidan Faransa ta ce a jiya Asabar kadai mutane dubu 50,000 ne suka fita a fadin kasar, idan aka kwatanta da mutane dubu 32, da suka fita a karshen watan Disamba, lokacin da zanga-zangar ta ja baya.

An dai samu arrangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro a wasu sassan kasar, ciki har da tsakiyar birnin Paris, inda wasu suka yi amfani da karfi wajen karya kofar shiga harabar ofishin kakakin gwamnatin Faransa Benjamin Griveaux, lamarin da ya tilastawa jami’an tsaro tserewa da shi.

A garin Bordeaux kuwa masu zanga-zanga dubu 4,600 suka fita inda kuma suka yi yunkurin yi wa ‘yan sanda rotse da duwatsu, su kuma suka maida raddi da hayaki mai sa hawaye da kuma ruwan zafi.

A halin yanzu dai ‘yan sanda 5 sun jikkata, yayin da ake tsare da masu zanga-zanga sama da 30 da aka kama a sassan kasar ta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.