Isa ga babban shafi
Faransa

Masu rigunan dorawa sun ci gaba da zanga-zanga a Faransa

Daruruwan masu zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Faransa sun sha alwashin yin fitar dango a wannan Asabar a birnin Versailles, domin ci gaba da kalubalantar sauye-sauyen da gwamnatin shugaba Macron ke kokarin aiwatarwa.

Masu zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Macron a Paris. 15/12/2018.
Masu zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Macron a Paris. 15/12/2018. REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Masu zanga-zangar da ke kiran kansu masu sanye da rigunan dorawa, sun soma yin tattaki a sassan Faransa tare da datse manyan tituna ne tun a tsakiyar watan Nuwamba, bayan da gwamnatin ta kara farashin albarkatun mai, wanda daga bisani suka tilasta mata janyewa.

Jami’ai sun ce ana sa ran akalla mutane 1, 400 ko sama da haka ne za su gudanar da zanga-zangar ta yau, duk cewa shugaba Macron ya sanar da karin albashin ma’aikata da kuma zaftare harajin da ake yankewa ‘yan fansho.

Zuwa yanzu mutane 9 suka rasa rayukansu a zanga-zangar ta kin jinin gwamnati, mafi akasarinsu sakamakon hadurran ababen hawa, zalika gidajen abinci da otal-otal sun tafka hasarar kudade masu yawan gaske, sakamakon tilast rufe su da zanga-zangar ta yi saboda fargabar tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.