Isa ga babban shafi
Faransa

Jami'an tsaro 600 a Faransa na farautar maharin Strasbourg

Akalla jami'an tsaro 600 aka baza a sassan kasar Faransa don farautar dan bindigar nan Sherif C da ya bude wuta kan daruruwan jama'a da ke tsaka da cinikayya a wata kasuwar kirsimeti ta birnin Strasbourg na kasar, inda ya hallaka mutane 3 ya kuma jikata wasu da dama.

Wasu 'yan Sanda lokacin da su ke rangadi a birnin Strasbourg na Faransa.
Wasu 'yan Sanda lokacin da su ke rangadi a birnin Strasbourg na Faransa. REUTERS/Vincent Kessle
Talla

Rahotanni sun ce yayin da ya ke kaddamar da harin, sojojin da ke samar da tsaro a kusa da wurin sun yi musayar wuta da shi, kuma sun raunana maharin amma kuma ya tsere.

Ministan cikin gida Christophe Castaner ya tabbatar da adadin mutanen da suka mutu, yayin da ya ce an kaddamar da gagarumin bincike domin gano inda dan bindigar ya shiga.

Castaner ya ce an daga matakin tsaron kasar da kuma karfafa tsaro akan iyakokin kasar da kuma samar da tsaro a daukacin kasuwannin krisimeti.

Wasu bayanai dai na nuni da cewa, dan bindigar ya yi kaurin suna wajen zaman gidan kaso bisa mabanbantan laifuka da suka hadar da fashi da makami.

Kawo yanzu dai hukumomin Faransa ba su bayyana harin da na ta'addanci ba haka zalika ba a sanar da kungiyar da Sherif ke yi wa aiki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.