Isa ga babban shafi
Birtaniya-Turai

Theresa May za ta yi murabus gabanin zaben Birtaniya na 2022

Firaministar Birtaniya Theresa May da ke fuskantar bore daga 'ya'yan Jam’iyyar ta konzabatib ta ce ba za ta jagoranci Jam’iyyar zuwa zaben shekarar 2022 ba, domin za ta sauka daga mukamin ta bayan kammala shirin ficewar kasar daga kungiyar kasashen Turai.

Firaminista Theresa May na ci gaba da fuskantar cikas a shirinta na ficewar Birtaniya daga EU matakin da ke sanya mata bakin jini hatta daga 'ya'yan jam'iyyarta.
Firaminista Theresa May na ci gaba da fuskantar cikas a shirinta na ficewar Birtaniya daga EU matakin da ke sanya mata bakin jini hatta daga 'ya'yan jam'iyyarta. Parbul TV/Handout via Reuters
Talla

Dan Majalisa Alec Shelbrooke ya shaidawa manema labarai cewar, May ta shaida musu haka kafin fara kada kuri’ar yankar kaunar da wasu ‘ya'yan jam’iyyar suka bukaci yi domin tantance goyan bayan da take da shi.

Wasu yan majalisun da suka hada da minista Amber Rudd da Robert Buckland duk sun tabbatar da matsayin Firaministar.

Yanzu haka dai Majalisar na kadawa Firaministar kuri'ar yankan kauna ne game da shirinta na fitar da kasar daga kungiyar Tarayyar Turai wanda ke ci gaba da fuskantar cikas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.